Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Maraba da Masu Saka Jari daga Kowace Kasa - Buhari


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaba Buhari yace Najeriya kasa ce da ta himmatu da matsalolinta amma kuma bata yi komi a kansu ba lamarin da ya hanata cigaba kamar yadda ya kamata

Yau Talata shugaba Buhari yake magana a fadarsa dake Abuja yayinda yake karban bakuncin shugabannin kamfanonin Afirka dake kira motoci da shugabansu Mr. Jeff Nemeth ya jagoranta.

Shugaba Buhari yace idan har zamu samu cigaba "dole ne mu gujewa kurakuran baya da gwamnatoci da ma kamfanoni suka yi" inji Buhari. Ya kara da cewa "yanzu ashirye muke mu karbi jari daga koina domin mu inganta rayuwar al'ummarmu".

Shugaba Buhari ya ciji yatsarsa saboda yadda kasar ta kasa samun cigaba wurin kero motoci tun lokacin da aka fara kirasu a Bauchi da Kaduna da Ibadan. Maimakon haka, sai kasar ta cigaba da dogaro ga man fetur a matsayin hanya daya tilo ta samun kudin shiga da kula da tattalin arzikinta.

Shugaban ya cigaba da cewa "muna kokarin sake gina ma'aikatar karafa saboda na ga damar dake akwai wa kasar da masu saka jari daga waje" inji shugaban..

Da yake mayarda martani, shugaban kungiyoyin, Mr. Nemeth yace kungiyoyin na cike da masu son saka jari kuma ashirye suke su yi hakan a yankin Afirka gaba daya.

Yace "ashirye muke mu hada hannu da Najeriya. Muna son mu inganta dokokin da ka iya karfafa saka jari da kamfanonin kire-kire da safara", inji Nemeth.

Zamu cigaba da inganta gine gine da kirkiro ayyuka da horas da kwararru", inji shi.

Shugaban kungiyoyin ya nemi goyon bayan gwamnatin Shugaba Buhari domin a cimma muradun kasar da na kungiyoyinsu.

XS
SM
MD
LG