Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kowane Dan Najeriya Nada Hurumin Zama Inda Ya Keso


Gwamnatin jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya, ta bayyana cewa ba ra'ayinta bane Fulani makiyaya su fice daga yankin kabilar Igbo, bayan wata kungiyar dattawan Arewa ta nemi Fulani makiyaya su bar kudancin kasar baki daya.

Mista Emmanuel Uzor, kakakin gwamnatin jihar ne ya fadi hakan a wata hirar da ya yi da Muryar Amurka akan batun, inda ya kara da cewa.

"Abin da muke fadi shine yankin kudu maso gabas da jihar Ebonyi na kowane, na duk kowane mai kaunar zaman lafiyane. Kuma a matsayinmu na al'umma, bamu taba gayawa wani cewa ya bar jihar Ebonyi ko wani bangarenta ba, saboda haka, bamu taba korar wani ba."

Mista Emeka Onah da Mista Ezealor Daniel Ezenyi wasu 'yan asalin kabilar Igbo ne, 'yan asalin jihar Inugu da Imo, suma sun bayyana ra'ayoyinsu game da batun.

Mista Emeka Onah ya ce, "Wannan bai dace ba a matsayinmu na al'umma, saboda ba wanda zai iya rayuwa shi kadai. Ficewar Fulani daga yankin zai kawo tsaiko ga tattalin arziki da ma rayuwa baki daya. Saboda haka, ya kamata a zurfafa tunani akan wannan batun.

Yayin da kuma Mista Ezealor Daniel Ezenyi ya ce, "Ina harkoki na a Arewa, ina fataucin tumatir, albasa daga Jihar Filato in kawosu nan in sayar. Saboda haka, kowa ya zauna duk inda yake ya gudanar da harkokinsa. Ya za a ce wani ya bar harkokinsa ya koma gida? Idan ya dawo, mai za'a bashi ya ci da kansa da iyalinsa? Wannan bai dace ba."

Su kuma Fulani makiyaya a yankin kudu maso gabas suke ganin wannan bashi da alheri a garesu, yayin da wannan dambarwar ke ci gaba? Alhaji Gidado Siddiki shine shugaban kungiyar Miyetti Allah a kudu maso gabas ya ce babu wanda yayi shawara dasu, akan komawa arewacin Najeiya, domin su suna zaman lafiya da kowa a inda suke.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG