Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shebab ta aiwatarda hukuncin kisa a kan wasu mutanen bisa zargin leken asiransu.


Mayakan Kungiyar Al-Shabab
Mayakan Kungiyar Al-Shabab

A wata sabuwa kuma, mayakan al-Shabab na kasar Somalia sun zartar da hukuncin kisa a kan mutane biyar ciki har da wani matashi mai shekaru 16 da suke masa zargin dan leken asiri ne na kasashen Kenya da Amurka da kuma Somalia.

An kashe matashin ne da sauran mutane hudun a gaban jama’a ta hanyar bindigesu a shekaranjiya Lahadi a garin Idale mai tazarar kilomita 60 daga kudancin Baidoa, bayanda wani alkalin kungiyar al-Shabab ya yanke musu hukunci kisa bisa amsa laifinsu da aka ce sun yi.

Al-Shabab dai ta kashe jumular mutane 22 a wannan shekara, tara a cikin an kasha su ne bisa zargin leken asiri kana saura kuma a kan laifukar da suka hada da fiyade da luwadi da kuma sama da fadi da dukiya.

Kugiyar mai alaka da al-Qaida tayi shekaru da dama tana yunkurin kifar da gwamnatin Somalia domin ta samu damar girka tsarin Shari’ar Islama akan kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG