Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Amnesty International Tace Sojojin Najeriya Sun Kashe Mutane 17


Sojojin Najeriya

Kungiyar Kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce sojojin Najeriya sun kashe akalla mutane 17 a lokacin wani gangami da ‘yan awaren kungiyar Biafra suka yi a kudu maso gabashin kasar.

Magoya bayan fafutukar ta Biafra, sun taru ne a birnin Onitsha da kewaye a karshen watan da ya gabata domin tunawa da ranar da yankin ya bangaren daga Najeriya na dan wani lokacin da bai yi tasiri ba.

Kungiyar ta Amnesty ta ce a ranar jajiberin aukuwar lamarin, sojojin Najeriya sun kai farmaki akan wata mujami’a inda masu fafutakar ta Bifara ke kwance, suka kuma bude wuta da harsashen gaske tare da harba hayaki mai sa hawaye akan daruruwan mutane, al’amarin da ya halaka mutum guda.

A cewar Amnesty, a washegari ne kuma sojoji suka harbi mutanen da suka taru a wani wajen jiran motar haya, inda nan ma suka bude wuta akan masu zanga zanga da suka rufe wata mahadar hanya a birnin na Onitsha tare da kashe wadanda ke wucewa.

Makmid Kamara, jami’i ne a kungiyar ta Amnesty, ya kuma ce wadanda aka bude musu wutar, ba sa dauke da makamai. yace “Muna ganin wadannan hare-hare daidai suke da kisan babu gaira ba dalili, sannan mafi yawan harbin da aka yi, an yi su ne na kan-mai-uwa- da-wabi.”

Sai dai dakarun Najeriya sun musanta wannan rahoto da kungiyar ta Amnesty ta fitar.

A wata sanarwa, sojojin na Najeriya sun ce masu fafutkar kafa kasar ta Biafra, sun yi arangamar da ta haifar da mutuwar ‘yan sanda biyu.

‘Yan kungiyar ta Biafra sun kuma ce akalla mutane 50 aka kashe musu, sai dai Amnestyn ta ce mutane 17 kawai ta iya tabbatar da mutuwarsu, amma ta ce ta yi imanin sojojin na Najeriya sun kwashe gawarwakin wasu da ga cikin wadanda suka kashe.

XS
SM
MD
LG