Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Hara Na Kara Kai Harin Sari Ka Noke a Adamawa


Mazauna kauyukan Adamawa na tserewa daga Boko Haram.
Mazauna kauyukan Adamawa na tserewa daga Boko Haram.

'Yan kungiyar Boko Haram na cigaba da kai harin sari ka noke kan wasu kauyukan karamar hukumar Madagali inda babu jami'an tasaro sai 'yan banga

Mayakan Boko Haram dake gujewa daka hare-haren da dakarun sojojin Najeriya ke kai masu a sansaninsu dake dajin Sambisa suna farke fushinsu kan kauyukan da basu da jami'an tsaro.

A karshen mako sun sake kai hare haren sari ka noke a wasu kauyukan karamar hukumar Madagali dake kan iyakan jihohin Adamawa da Borno.

Mayakan sun kai hari a kauyukan Sabongari da Dutse Biyu kuma kawo yaznzu ba'a tantance adadin wadanda aka kashe ba. Maharan suna fakewa ne cikin duwatsu da dazukan dake kewaye da yankin.

Sakamakon karancin jami'an tsaro a yankunan da sojoji suka kwato 'yan banga ne suke taka muhimmiyar rawa wajen kare yankunan.

Al'ummar yankin na rokon gwamnati da ta kai masu doki cikin gaggawa. Wani ganao yace bayan maharan sun bar Sabongari sun farma Kafin Hausa inda suka yi kashe kashe tare da kone gidaje.

Kazalika dan majalisa dake wakiltar yankin ya sake tabbatar da kashe mutane ba iyaka tare da kone gidaje. Saboda haka ya kira gwamnati ta jibge sojoji a yankin.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG