Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Sake Kai Hari a Yankin Madagali dake Jihar Adamawa


Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a Kuda dake yankin Madagali, cikin jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar,inda suka kona gidaje da sace abinci kamar yadda suka saba yi a 'yan kwanakin nan.

Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a Kuda dake yankin Madagali, a jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya

Yankin Madagali yana gaf da bakin dajin Sambisa inda 'yan ta'addan Boko Haram suke samun mafaka. A wannan harin, kamar yadda suka saba yi a yankin, sun kone gidaje, kaddarori tare da sace abinci

Wannan nema hari na kusan tara a kasa da makwanni biyu da 'yan Boko Haram ke kaiwa yankin na Madagali kusa da dajin Sambisa tungar 'yan bindiga masu tada kayar baya.

Rahotanni dai sun bayyana cewa an kai wannan sabon harin ne a kauyen Kuda inda suka yi kone-kone da kuma diban abinci,koda yake kawo yanzu ba’a tabbatar da alkalumman wadanda lamarin ya shafa ba.

A yanzu dai, ba kasafai hukumomin tsaro ke yin bayani kan irin wadannan hare haren da ake kaiwa ba, amma kuma shugaban karamar hukumar Madagalin Yusuf Muhammad ya tabbatar da faruwan lamarin inda ya bukaci shugaba Buhari da ya haska fitillarsa kan abubuwan dake faruwa a wadannan yankunan da aka kwato.

Wadannan sabbin hare haren dai,na zuwa ne a yayin da masana da kuma kungiyoyin kare hakkin bani Adama,ke kiran da a binciKI yadda ake gudanar da yaki da Boko Haram.

Barrister Sunday Joshua Wigra wani lauya mai zaman kansa,yace akwai bukatan karatun ta natsu.

Kawo yanzu dai duk kokarin ji daga rundunan ta 28 dake Mubi,wato 28 Task Force ya citura kasancewar yanzu an maidasu karkashin rundunan dake Chibok ne.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG