Accessibility links

Kungiyar Boko Haram tayi barazanar hambarar da gwamnatin Nigeria

  • Jummai Maiduguri

Wasu mutane ne suka taru kusa da inda bam ya tashi a Kaduna a kwanan nan.

Mutumi dake ikirari cewa shine shugaban kungiyar Boko Haram yace cikin watani uku zai hambarar da gwamnatin shugaba Jonathan

Mutumin dake ikirari cewa shine shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau yace cikin watani uku zai durkusar da gwamnati shugaba Jonathan.

Wani hoton vidiyo na mintoci goma sha hudu da aka sa a duniyar gizo ya nuna wani mutum da aka gabatar cewa shine Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram, yana ba'a da alkawarin da shugaba Jonathan yayi makoni biyu da suka shige cewa, kan tsakiyar wannan shekara, idan Allah ya yarda za'a samu damar magance matsalar tsaro a Nigeria.

Shi wannan mutumin dake cikin hoton vidiyon wanda ke kewaye da mukarabansa dauke da makamai yayi magana ne da Hausa. Yace kunji sakon da shugaba Jonathan ya gabatar cewa cikin watani uku in Sha Allahu za'a ga bayan yan kungiyar Boko Haram. Yace babu wanda zai bigi kirji yayi wannan furuci, sai wanda ya raina mahalicinsa.

Ba'a dai tabbatar da sahihanci hoton vidiyon daga wata kafa ta fisabillahi ba. Ana ta dai samun karuwar hare haren yan kungiyar Boko Haranm a arewacin Nigeria, kungiyar da aka dorawa alhaki kashe daruruwan mutane a bana kurum.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG