Accessibility links

Mutane 7 sun mutu a hare-haren bama-bamai a Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Gawar wani da harin bam din da aka kai Kaduna ya rutsa da shi

Jami’ai sun ce wani harin bam din da aka kai a wani gidan jarida a babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja ya hallaka mutane 3

Jami’ai sun ce wani harin bam din da aka kai a wani gidan jarida a babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja ya hallaka mutane 3, a sa’ilinda wata fashewar kuma daura da ofishin jaridar a birnin Kaduna da ke arewacin kasar ta hallaka wasu mutanen kuma su hudu.

Jami’an sun ce fashewa ta farko a yau Alhamis ta auku ne a ofishin jaridar This Day da ke birnin Abuja, wadda daya ce daga cikin shaharrun jaridun Nijeriya. Ciyaman din kwamitin tsare-tsaren rubutun jaridar, Olusegun Adeniya, ya ce wani dan kunar bakin wake ne ya abka ta mashigar ginin da wata mota samfurin jeeb. Ya ce harin ya yi sanadin kashe wasu masu gadi biyu da maharin.

Wani wakilin Muryar Amurka da ke wurin da abin ya faru ya ce cincirindon mutanen da su ka taru bayan harin ciki da matukar fushi, sun yi ta ihu su na cewa “sam babu tsaro a Nijeriya.”

A halin da ake ciki kuma, wani wakilin Muryar Amurka ya fadi a Kaduna cewa ‘yan sanda na rike da wani wanda ake zargi bayan da bam ya tashi da daura da wani ginin da ya kunshi ofishin jaridar ta This Day da wasu jaridun kuma biyu – “The Moment” da kuma “The Sun.” Hukumomi sun ce fashewar ta yi sanadin mutuwar mutane 4 tare da raunata wasu da dama.

Wani mazaunin garin Kaduna Diji Obadiah ya ce maharin ya abka wa ginin da ya kunshi ofishin jaridar da motarsa, a daidai lokacin da ya ke ta cewa “Allahu alkbar.”

Obadiah ya ce mutane sun so su kashe maharin da duka bayan da ya dauko wani bam daga cikin motarsa ya jefa kan cincirindon jama’a.

Nan take dai babu wanda ya dau alhakin kai harin.

Yau shekaru biyu kenan hukumomi na kokarin tsayar da yawan hare-haren bama-bamai da harbe-harbe a arewacin Nijeriya, wadanda akasari akan dora alhakin aikata su ne kan tsattsaurar kungiyar Islama ta Boko Haram.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG