Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar IGAD Ta Ce Shugaban Sudan Ta Kudu Da Mataimakinsa Su Kwashe Sojojinsu Baki Daya Daga Babban Birnin Kasar


Kungiyar bunkasa yankin gabashin Afrika ta IGAD, ta ce ya kamata sojojin kiyaye zaman lafiya nata su karbe ayyukan kula da tsaron Juba daga hannun dakarun shugaba Salva Kiir da na mataimakinsa Riek Machar dake gwabzawa da junansu.

Kungiyar bunkasa yankin gabashin Afrika ta IGAD, ta yi kira ga dakarun da ke marawa shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir da kuma mataimakinsa Riek Machar baya, da su fice daga birnin Juba, domin a maye gurbinsu da wasu dakarun kungiyar da za su kula da harkar tsaro.

Ministan harkokin kasashen wajen kasar Uganda, Okello Oryem, ya ce kungiyar ta IGAD ta yi wani zama a gefen taron kolin kungiyar tarrayar Afrika da ke gudana a Kigali, inda ta nuna goyon baya ga shawarwarin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon kan kara karfafa shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

A wata sanarwa da ya fitar a karshen makon da ya gabata, Ban Ki moon, ya yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar da ya kakaba takunkumi hana sayen makamai akan Sudan ta Kudu, da wasu shugabannin kasar da kwamandoji da suke kawo tarnaki a shirin zaman lafiyan, sannan a kara karfafa shirin wanzar da zaman lafiyar majalisar na UNAMISS a Sudan ta Kudu.

Ban ya kuma kara da cewa duk wani shirin maido da gudanar da gwamantin hadaka a kasar, zai dogara ne akan janyewar dakarun bangarorin biyu daga Juba.

XS
SM
MD
LG