Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masalaha Nada Wuya A Sudan ta Kudu -Bube Namaiwa


Mayakan 'yan tawayen Sudan ta Kudu

Yau shekaru biyar ke nan da Sudan ta Kudu ta yanke daga kasar Sudan ta zama kasa mai cin gashin kanta to amma tafiya bata yi nisa ba sai rikicin kabilanci ya barke cikin wannan sabuwar kasar lamarin da ya kaiga yakin basasa da yanzu ya kwashe fiye da shekaru biyu.

Ganin yadda ake ta kai-komo a kasar Sudan ta Kudu, Muryar Amurka ta zanta da Farfasa Bube Namaiwa, shehun malami a jami'ar Ahmadu Diof dake kasar Senegal domin ya yi fashin baki akan wannan lamari mai daure kai.

Da aka tambayeshi ko za'a iya samun masalaha a kasar sai Farfasa Bube Namaiwa yace akwai wuya. Amma fatansu shi ne su samu zaman lafiyan.

Yace dama can a zamanin da suke cikin kasar Sudan makiyi guda garesu, wato mutanen arewacin Sudan din. Da suka samu 'yancin kai sai suka koma kan junansu da kiyayya. Idan aka koma tarihi, tun kafin a turasu cikin kasar Sudan akwai kabilu da basa jituwa da juna. Tun a zamanin suna zaman yaki ne. Yanzu wannan tsohuwar kiyayya dake tsakaninsu ce ta sake kunno kai.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Tsohuwar gabar ce ta sa Salva Kiir da Machir kowanensu yana son ya zama sarki. Saboda haka akwai wuya a ciwo kan gabar dake tsakaninsu. John Garang ne kadai ya iya rikesu duka amma tunda ya rasu kawunansu suka rabu bisa kabilanci. Yanzu kowa ya tayar da kayar baya.

Samun zaman lafiya a kasar ya rataya ne akan Majalisar Dinkin Duniya ko MDD da Amurka domin su ne suka yi ruwa da tsaki wajen ganin an kirkiro Sudan ta Kudu.

Da ana ganin fadan tsakanin musulmin arewacin kasar ne da kiristocin kudancin ita tsohuwar Sudan din ne lamarin da ya sa duk wani kirista ya goyi bayan kirkiro Sudan ta Kudu. Yau gashi kasar ta samu 'yanci amma bata da zaman lafiya. Ke nan ya zama wajibi kan duk wadanda suka dage sai Sudan ta Kudu ta balle su tabbatar da zaman lafiya.

Bube Namaiwa na ganin abun da ya fi a'ala ga Afirka shi ne a samu kasashe hudu kawai. Wato duk kasashen yammacin Afirka su dunkule su zama daya. Haka ma na arewanci su zama daya. Na gabashin nahiyar su zama daya .Na kudanci kuma su zama daya.

Yayi misali da Najeriya. Yace da yankin dake kiran kansa Biafra ya balle da yanzu duk kabilun wurin sun barke da fada da babu kasar. Kasancewarsu a Najeriya ya basu zaman lafiya da cigaba.

Babban daratsi da ya kamata a koya shi ne rungumar juna a zauna tare kamar yadda kasashen turai suka hada kansu. A yi koyi da Amurka wadda ta hada kanta. Kasashen Indiya da Brazil duk sun hada kawunansu domin gina kasa daya.a yankunansu.

Kafin kasashen Afirka su cigaba sai sun cire kabilanci da addini a harkokin siyasa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:36 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG