Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar CIRAC Ta Nuna Damuwa Kan Tabarbarewar Tsaro a Jamhuriyar Nijar


Jami'an kwanta da tarzoma a Nijar

Kungiyar tsofaffin Ministoci da manyan jami’an diflomasiya na Jamhuriyar Nijar ta yi kira ga hukumomi da su farka daga barci don tunkarar matsalar tsaro dake kara tsananta a jihar Tilabery, inda yanzu haka dubban mazauna garuruwan da ke kusa da iyakar Mali suka fara tserewa daga matsugunnansu.

A wata sanarwar da suka fitar a karkashin inuwar kungiyarsu ta CIRAC, tsofaffin jami’an da suka shafe shekaru da dama wajen kare martabar Nijar, sun nuna damuwa a game da yadda ayyukan ta’addanci ke kara tsananta kusan a kowacce rana.

Halin da ake ciki a yau bayan shafe shekaru da dama na yaki da kungiyoyin ta’addanci a Nijar, ya sa kungiyar CIRAC aza ayar tambaya dangane da tasirin matakan da hukumomi ke cewa suna dauka da nufin tunkarar matsalar tsaro.

Dubun dubatar sojojin kasashen waje wadanda galibinsu na yammacin duniya ne ke girke a yankin Sahel da sunan yaki da ta’addanci, amma kuma bayanan da ke fitowa daga fagen daga na nuni abin yana neman ya gagari kundila.

Kungiyar CIRAC a wannan sanarwa ta zo da wasu shawarwarin da take ganin ita kadai ce mafitar ta’asar da ‘yan bindigar arewacin Mali ke tafkawa a jihar Tilabery.

Saurari cikakken rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00


Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG