Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamarin Masar Abun Bakin Ciki Ne - in ji Manazarta


Adli Mansour babban alkalin kotun koli na Masar, wanda aka rantsar da shi yau, kwana daya kennan bayan da sojoji suka rushe gwamnatin Mohammed Morsi.

Sojoji sun hambarar da shugaban demokradiyya na farko a kasar Masar, kuma sun rantsar da shugaban rikon kwarya yau kwana daya kennan, kuma wannan lamari, ya samu tsokaci iri-iri daga manazarta da kwararru a harkokin siyasa.

Dr. Shehu Dalhat na jami'ar bayero dake Kano a Najeriya, ya bayanna ra'ayoyinshi ga Jummai Ali na sashen Hausa.

Yace: Abun bakin ciki ne, kuma ci baya ne ga cigaban demokradiyya a Afrika da duniya baki daya, kuma wannan ya nuna iya karfin ikon da sojoji suke da shi a harkar siyasa da sauran lamura da suka shafi yau da kullum.

Dr. Dalhat ya cigaba da cewa: Wannan yana da tasiri sosai ga harkar siyasa baki daya a Afrika, musamman idan aka fahimci cewar bukatun jama’a sune bukatu, mutane sun kawo korafe-korafe da yawa, da kuma sakaci da rashin iya aiki daga wannan shugaban kasa da aka kore.

Jummai ta tambaye shi: Idan akayi la’akari da abubuwan da suka faru a masar din a shekara daya da yayi, bai yi kadan ba domin mutane su ga abinda suke so ba?

Mr. Dalhat yace: I, gaskiya ne shekara daya yayi kadan, amma an ce juma’a mai kyau, tun daga Laraba take farawa. Mai makon ya nuna wa mutane muhimmancin dimokradiyya, tsarin da ya dauko zai dauki lokaci kafin a samu cigaban da ake bukata. Kuma mutane suna da gaggawa, mutane basu da hakuri, sun manta da cewa an dade ana mulkin kama karya a Masar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG