Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Hattara Da Matakan Tsaro Da Take Dauka - Masana


Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

A Najeriya bisa ga yadda hukumomi a jihohin Arewa ke kakaba dokoki domin neman sauki ga matsalar rashin tsaro, wasu ‘yan kasar na ganin a yi farautar ‘yan bindigar a gama da su zai fi kakabawa mutane dokoki.

Masana lamarin tsaro sun bayyana cewa idan tura ta kai bango, akan dauki kowane irin mataki muddin ana sa ran zai kawo sauki ga matsalar rashin tsaro.

Wannan bai rasa nasaba ga yadda gwamnoni a yankin Arewa ke kakaba dokoki a jihohinsu, don ganin an samu mafita.

Kwamishinan yada labarai na jiha Sokoto Isa Bajini Galadanci ya ce gwamnatin jihar ta bi takwarorinta wadanda suka saka irin wadannan dokokin.

Jihar ta Sokoto ta hana daukar mutum uku akan babura da kan keke-napep a duk fadin jihar.

Sauran dokokin sun hada da hana zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a cikin gari da kuma 6 zuwa 6 a yankunan da ke da matsala.

Sannan an hana kasuwancin dabbobi a garuruwa masu matsalar tsaro, da hana motoci shiga daji su dauko itace, da cinikin babura da taba-jiki a yankunan da ke da matsalar.

Masana lamurran tsaro na ganin cewa wadannan dokokin sun yi amma idan suka dauki dogon lokaci wata matsala na iya sake kunno kai.

Wadannan dokokin sun fara aiki daga daya ga watan Satumba, sai dai kuma an yi sassauci ga ma'aikatan da ke ayukka na musamman.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Hattara Da Matakan Tsaro Da Take Sakawa - Masana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00


XS
SM
MD
LG