Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Kasa Ta Bukaci CBN Ya Wadata Jama'a Da Sababbin Kudi Ko Ya Fito Da Tsofaffi


Shugaba Buhari, hagu, da tsoffin shugabannin Najeriya
Shugaba Buhari, hagu, da tsoffin shugabannin Najeriya

A ranar Juma’a majalisar ta yi wani taron gaggawa don tattauna halin da kasa ke ciki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Majalisar kasa a Najeriya, ta bukaci babban bankin CBN da ya buga karin sababbin takardun kudi, ko kuma a fito da tsofaffin da ake amfani da su don a rage radadin wahalar da jama’a ke fuskanta.

Majalisar wacce ke karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta hada da tsofaffin shugabannin kasar, gwamnoni, shugabannin majalisar tarayya da kuma ministoci.

A ranar Juma’a majalisar ta yi wani taron gaggawa don tattauna halin da kasa ke ciki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Batutuwan da suka dauki hankali a taron sun hada da wahalar da ake fuskanta a kasa saboda sauyin kudin naira da kuma zaben 2023 da ke tafe.

‘Yan Najeriya na fuskantar wahalhalu iri-iri wajen cire kudadensu a bankuna tun bayan da aka fitar da sababbin takardun kudi na 200, 500 da 1000 da aka sauyawa fasali.

Babba bankin na CBN ya ce wasu ne suke boye sababbin kudaden don amfanin kansu.

Sai dai a zaman da majalisar kasar ta yi, an bukaci CBN da ya himmatu wajen buga karin sababbin kudaden don mutane su wadata.

A gefe guda, majalisar kasar ta nuna goyon bayanta ga sauya fasali da aka yi wa kudaden.

Daga cikin tsoffin shugabannin da suka halarci taron akwai Janar Yakubu Gowon mai ritaya, Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya sai Goodluck Jonathan.

XS
SM
MD
LG