Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Cafke Birnin Ramadi a Iraaqi


Mayakan ISIS.

Kungiyar ISIS tayi ikirarin cafke birnin Ramadi dake da tazarar kilomita 125 daga babban birnin Baghdad fadar gwamnatin Iraqi

Jiya Lahadi kungiyar ISIS tayi ikirarin cafke babban Birnin Ramadi dake kasar Iraqi. Cafke Birnin shi ne nasara mafi mahimmanci da kungiyar ta samu a wannan shekarar bayan tayi kwana da kwanaki tana gwabza kazamin fada da dakarun Iraqin.

A nan Washington hedkwatar tsaron Amurka ta ki ta tabbatar da ikirarin da kungiyar ta yi tana cewa akwai shakka.

To saidai wasu da suka hada da mai magana da yawun gwamnan yankin Anbar sun ce dakarun gwamnati suna arcewa daga Birnin.

Tun farko Firayim Ministan Iraqi ya gargadi sojojin kasar kada su bar filin daga amma hada gwiwa da mayakan sa kai na ‘yan Shi’ait su kwato Birnin.

Duk da hare-hare ta sama da Amurka da kawayenta ke kaiwa kan yankin, kungiyar ISIS ta sha kutsawa yankin har ta cimma cafke yawancin Birnin Ramadin.

Cafke Birnin da kungiyar ISIS ta yi ya sa tana da tazarar kilomita 125 daga Birnin Baghdad fadar gwamnatin Iraqi.

Tun ranar Juma’a kungiyar ISIS ta daga tutarta a ginin gwamnatin karamar hukumar yankin.

Bayan da ta daga tutarta ta cigaba da tayarda bamabamai har jiya Lahadi inda ta kashe sojoji goma da ‘yan sanda masu yawa.

To saidai kuma a wata sabuwa ita kungiyar ta samu koma baya. Dakarun Syriya sun samu nasarar dakatar da mayakanta daga shiga tsohon Birnin Palmyra mai dimbin tarihi. Dakarun Syria sun kashe mayakan da dama.

Birnin Palmyra yana da wuraren tarihi dake karkashin Kungiyar Kayutata Ilimi da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya.

XS
SM
MD
LG