Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: 'Yan takarar Republican Sun Baje Koli a Iowa


'Yan takarar neman shugabancin kasar Amurka a zaben a shekarar 2012 a jahar Iowa

Masu neman takarar shugabancin Amurka daga jam’iyyar Republican su 11, sun yi wani taro jiya Asabar a Jahar Iowa da ke tsakiyar Amurka, domin su gayawa kusoshin jam’iyyar da ke jahar, dalilin da ya sa kowane dayansu ya ke ganin shi ya fi cancanta a zaba a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Reshen jam’iyyar ta Republican a jahar ta Iowa ne ya dauki nauyin wannan taro, inda aka karkata hankali kan batutuwan da suka shafi Iran da Musulunci da kuma rikicin da ake samu a Gabas ta Tsakiya.

Dukkanin ‘yan takarar, sun yi kiran cewa Amurka ta kasance tana ko ina a duniya, sai dai sun banbanta kan irin tsaurin da kasar ya kamata ta dinga nunawa akan makiyanta.

A lokacin da aka tambayi tsohon Sanata Rick Santorum kan yadda za a bullowa batu Iran, sai ya ce “mu daura damarar bama-bamai kawai a tunkudasu su koma karni na bakwai,” yayin da shi kuma Sanata Rand Paul ya dasa alamar tambaya, shin ko ma ya dace da aka mamaye Iraqi, ganin yadda kungiyar ISIS ke ci gaba da samun karbuwa.

Wasu daga cikin ‘yan Republican din dai sun dora alhakin bunkasar da kungiyar ta ISIS ta samu ne akan shugaba Barack Obama, saboda a cewarsu, ya ki barin dakaru a baya a kasar Iraqi, bayan da sojojin Amurka suka janye.

Sun kuma soki mai neman takara a karkashin jam’iyyar Democrat, Hillary Clinton, kan rashin amsa tambayoyin masu kada kuri’a a lokacin yakin neman zabe.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG