Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Tabbatar da Mutuwar Wani Babban Shugabanta


Inda aka kashe Abu Mohammad al-Adnani shugaban kungiyar ISIS
Inda aka kashe Abu Mohammad al-Adnani shugaban kungiyar ISIS

Kungiyar ISIS ta tabbatar cewa an kashe daya daga cikin manyan shugabaninta, kuma kakakin kungiyar Abu Mohammed al-Adnani, sa'ilinda aka kai hari kan motar d a yake ciki yayinda take tafiya a yankin da ake kira al-Bab a arewa maso gabashin Aleppo

. Rahotanni suna nuni da cewa ya gamu da ajalinsa ne sakamkon wani hari da Amurka ta kai da jiragen yaki, amma jami'an tsaron Amurka suna cewa sun auna harin ne kan wani babban jami'in kungyar ISIS.

Ahalinda ake ciki kuma, babban kwamandan cibityar kula da yake yaken da Amurka take yi Janar Joseph Votel, ya bayyana farin cikin Amurka kan kutsen da Turkiyya ta kai ta kan iyakar kasar da Syria ind a ta auna kungiyar ISIS, ya kira kutsen da turkiyyar ta kai makon jiya, 'muhimmi kuma wani iri daban abunda Amnurka tayi lale da shi.' Haka nan Kwamandan na Amurka yace yana mutunta irin gudumawarda wata kungiyar 'yan tawaye a Syria da ake kira SDF a takaice take bayarwa, ciki harda kurdawa wadanda a cewarsa-muhimman kawaye ne a yaki da ake yi da ISIS.

Da take magana kan kutsen data kai, Turkiyya tace ba zata tsaida farmakin da ta fara makon jiyan a, har sai ta kawarda duk wata barazana.

A makon jiyan ne Turkiyya ta kadsamar da hare haren wadnda ta auna kan kungiyar ISIS, da kuma mayakan sakai na kurdawa da suke samun goyon bayan Amurka, wadanda Turkiyyan take dangantawa da kungiyar PKK ta 'yan tawayen kurdawan wacce ta juma tana fafatawada gwamnatin kasar.

Arangama tsakanin Turkiyya da kurdawan ya sake dama yanayi wanda tuni yake cike da sarkakiya a Syria-inda gwanatin kasar take samun goyon bayan Iran, da Rasha, da kuma kungiyar mayakan sakai ta Hezbollah mai cibitya a Lebanon, yayinda Amurka da wasu kasashen yammacin duniya suke goyon bayan 'yan tawayen kasar.

"Sai kungiyoyin 'yan ta'adda, da duk wata barazana mun kau dasu, daga kan iyakokinmu da duk wani hadari ga 'yan kasan nan,kamin mu dakatar da wannan mataki," PM Turkiyya Binali Yildrim ya gayawa manema labarai.

XS
SM
MD
LG