Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mataimakin Shugaban Kungiyar IS Na Lardin Aleppo


Birnin Aleppo
Birnin Aleppo

Rahotanni daga Syria na nuni da cewa, an kashe mataimakin shugaban kungiyar IS na lardin Aleppo, wanda yayi aiki a matsayin kakakin kungiyar, da daukar sojojin haya, da kuma kai hare hare a kasashen turai.

Kungiyar IS ta sanar da mutuwar Abu Muhammad al-Adnani jiya Talata, lokacin yana sa ido kan ayyukan kungiyar na shawo kan hare haren sojin da ake kaiwa a Aleppo.

Wani babban jami’in tsaron Amurka yace dakarun hadin guiwa sun kai farmaki jiya talata da safe da jiragen sama a al Bab na kasar Syria kan shugaban kungiyar. Bai fadi ko an kai harin kan Adnani bane ko kuma an kashe shi. Yace jami’an Amurka suna kan nazarin sakamakon farmakin.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tayi tayin bada tukuicin dala miliyan biyar ga duk wanda zai bada bayanan da zasu kai ga kama Adnani.

Jami’an gwamnati a Washington sun shaidawa Muryar Amurka cewa, amurka ta gano manyan kungiyar IS da dama a lardin Aleppo, sai dai basu bada tabbacin ko Adnani na daya daga cikinsu ba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG