Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta “Human Rights Watch” tayi gargadin jami’an tsaron Nigeria ka iya wuce gona da Iri


Yan sanda na kaiwa da komowa a wajen wata kotun shari'a inda ake shari'ar wadanda ake zargi nada hannu wajen shirya tarzoma kafin a fara sauraren shari'arsu a Kaduna, Nigeria.

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya bada umarnin tura Karin jami’an tsarozuwa jihohin da ake tashin hankalin day a biyo sakamakon zaben shugaban kasa. Amma kungiyar kare hakkin Bil Adama ta “Human Rights Watch” tace ayi hattara domin jami’an tsaron Nigeria an sansu da wucegona da iri.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch da cibiyarta ke Amurka, ta gargadi shugabannin Nigeria da su tabbatar da ganin jami’an tsaron da za’a tura domin shawo kan zanga-zangar da ta biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasa a Nigeria basu wuce gona da irin ba wajen take hakkin Bil Adama. Shugaban Nigeria Goodluck Jonthan ya bada umarnin tura Karin jami’an tsaro zuwa jihohin Arewa inda ake rikicin da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasar da aka bayar. Masu tarzoma sun kona gidaje da kadarori domin huce fushinsu. Shugaban na Nigeria yana mai cewa abin bakin ciki ne ganin yadda wasu maras sa mutumci ke yin watsi da ‘yancin salon mulkin demokuradiyya ya tanadarwa al’umma, suka zama gungun masu tada fitina da tarzoma a kasa inda a wasu sassan Nigeria suka rika tada husuma suna karkashe jama’a da tozarta masu kaunar zaman lafiya, suka rika kone-konen gidajen jama’a da kadarori harda wuraren ibada, haka ba dai dai bane.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta “Human Rights Watch” tayi gargadin jami’an tsaron Nigeria ka iya wuce gona da Iri
Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta “Human Rights Watch” tayi gargadin jami’an tsaron Nigeria ka iya wuce gona da Iri

Waje daya kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar hamayya ta CPC Janar Muhamadu Buhari wanda aka kayar a zaben shugaban kasar na Nigeria yayi kukan cewar an tafka magudi a zaben na shugaban Nigeria amma duk da haka yace ba ba dai dai bane a tada tarzoma a kasa ba, don haka yayi kira ga magoya bayansa da su kai zucciya nesa suyi hakuri domin jam’iyyarsa zata je kotu ta kalubalnci sakamakon zaben. Sai dai shugaba Goodluck Jonathan yaci gaba da nuna yatsa ga masu tada hargitisn siyasa inda yake gaya masu cewa ya zama wajibi a tashi tsaye domin gano wadanda ke haddasa fitina a kasa domin su fuskanci hukunci, domin ba za’a zuba ido a kyalesu suna ci gaba da tada zaune tsaye a Nigeria ba.

Kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross tace zancen nan da ake yi tarzomar ta janyowa mutanen da yawansu ya kai dubu arba’in sun rasa muhallinsu, kuma ya zama wajibi Gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan tayi taka tsantsan ta kuma tabbatar jami’an tsaron da ake turawa domin murkushe masu zanga-zangar basu wuce gonad a iri ba wajen tauye hakkin al’umma. Babban jami’in Red Cross a Nigeria Eric Guttschuss yayi gargadin cewa an riga

san halin jami’an tsaron Nigeria wajen wuce gona da iri musamman idan suka sami umarni daga sama, sais u nemi take hakkin Bil Adama musamman a lokutan tashe-tashenhankulan addini ko na kabilanci. Kafofin labarum Nigeria sun ce akalla rikicin siyasar ya janyo halaka mutane dari amma Gwamnatin Nigeria tayi gum wajen bayyna yawan wadanda suka rasarayukansu a dalilin rikicin siyasar.

XS
SM
MD
LG