Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Limaman Kasar Kamaru Ta Gudanar Da Taron Addu'oi Na Musamman


kungiyar malaman addinin Mulunci ta kasar Kamaru (sidumuk) sun gudanar da addu’ar zaman lafiya a birnin Yaonde karkashin shugaban limamai na kasar Dr Musa Umaru.

Kungiyar ta gayyaci dukkan limaman ta dake babban birnin Yaonde, domin gudanar da addu’ar zaman lafiya kasancewar irin matsalolin dake nema su bijirewa kasar, musamman yadda ‘yan boko haram suka addabi jihar Arewa mai nisa, da kuma matasalar ‘yan awaren kasar da suke neman wargaza kasar gida biyu.

Daga gabashin kasar kuma ‘yan tawayen kasar Bangi ne suke kwararowa cikin kasar kamar yadda shugaban limamn kasar Dr Musa Ummaru ya bayyana yayin da yake karin bayani akan dalilin taron da kuma manufofinsu.

Alaramma sheik Ahidjo Ali, shine babban limamin birnin cinikayyar kasar jamhuriyar Kamaru, ya bayyana cewa wannan taro kamar yadda kungiyar hada kan limaman kasar ta shirya, an gudanar da shi ne da zummar yin addu’oi domin irin matsalolin da kasar ke ciki.

Domin karin bayanio saurari rahoton Muhamman Awal Garba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG