Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Malaman Najeriya Reshen Jihar Kano ta Bukaci 'Yan'yanta Su Zauna Gida Sai Gwamnati ta Samar da Naurorin Gwada Ebola


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Ranar Juma'a da ta gabata kungiyar malaman Najeriya reshen jihar Kano ta bukaci duk 'ya'yanta malamai dake koyaswa a makarantun firamare da sakandare kada su koma aiki har sai gwamnati ta samar masu da naurorin gwada cutar ebola.

Kungiyar tace kada su koma bakin aiki a dukannin makarantun firamari da sakandare muddin gwamnatin jihar Kano bata samar da naurorin gwaji da sauran kayan aiki na yakar cutar ebola ba.

Lawal Audu Garin Malam shugaban kungiyar a Kano yace matakin umurni ne daga hekwatarsu dake Abuja. Yace an ce a tanadi duk wani abu da zai kawo rigakafi ga yaro da malami. Dalili ke nan suka zauna suka tattauna kana suka yanke shawarar cewa malamai su zauna a gida har sai an basu kayan rigakafin.

Wannan matakin da kungiyar malaman ta dauka ya tilastawa gwamnatin jihar Kano kiran taron gaggawa na masu ruwa da tsaki akan harkokin ilimi. Daraktan hukumar dake kula da malaman sakandare na jihar Kano Habibu Hassan El-Yakub yace su a fuskar gwamnati sun yi iyakar kokarinsu. Sun horas da malamai dubu ashirin da hudu da dari bakwai. Sun horas dasu akan tsaftar yara.

Akan ko iyaye da dalibai zasu cigaba da dakon gwamnati ke nan har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta samar da naurorin ke nan, sai yace kwarai haka lamarin yake. Akan ranar da yara zasu koma sai yace an yi bayyani. An ce sai bayan sallah wanda ka iya zama ko bayan salla da kwana daya ko biyu. Yawancin jihohi ma sha uku ga watan Oktoba suka ce dalibai zasu koma makarantunsu.

Amma Lawal Audu Garin Malam yace su dai abun da suke bukata shi ne su ga kayan babu ruwansu da kowace gwamnati zata samar da kayan.

Dangane da horon da gwamnatin jihar Kano tayi ikirarin baiwa malaman makaranta fiye da dubu ashirin da hudu daya daga cikin wadanda suka samu horon cewa yayi ba horaswa aka yi masu ba an dai yi masu bita. Idan an ba mutum horo za'a bashi cikakke, a nuna masa tsarin da zai bi a gwada masa ya kuma jaraba ya gani. Amma basu ga komi ba a zahiri. Duk abun da suka gani a majigi aka nuna masu. Basu ga naurar ba basu kuma riketa babalantana su gwada.

Iyaye sun ce su basu ji dadi ba domin tuntuni ya kamata yara su koma makaranta. Zaman gidan da yara keyi ba alfanu ba ne garesu domin zasu rasa abubuwa da dama. Karatun yaran shi ne cigaban rayuwar iyaye.

Su ma daliban da aka zanta dasu sun ce zamansu a gida bashi da anfani. Suna son su koma makaranta.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG