Accessibility links

Kungiyar Matasan Kiristoci da Musulmai ta Shirya Taron Zumunci


Wasu matasa

Daidai lokacin da a ke yin bukukuwan karshen shekara kungiyar matasan Kiristoci da Musulmai ta shirya taron karfafa zumunci tsakanin addinan biyu.

A daidai lokacin da ake bukukuwan karshen shekarar 2013 kafin a shiga shekarar 2014 kungiyar matasan Kiristoci da Musulmai ta shirya taron kara fahimtar juna domin karfafa zumunci musamman a arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar Yusuf Ibrahim ya bayyana manufofi ko kuma hujjojin shirya taruruka a dai dai wannan lokacin. Musulmai da Kirista su zo su zauna tare su tattauna kan abubuwan da zasu kawo cigaban kasar. Bayan sun gama tattaunawa zasu yi biki domin kowa ya ji dadi kafin su kama hanyar gidajensu. Makasudin abun da ya sa suke yin irin wannan taron da shirya bukukuwa lokacin bikin kowane addini shi ne tashin hankalin da aka samu da a kasar tsakanin mabiya addinan biyu. Ya ce bayan sun zauna sun yi bincike kan musabbabin abun dake haddasa tashin hankali sai suka gane cewa siyasa ce take kawo tashin hankali. Ya ce idan an lura daga karshen taron siyasa sai a kawo batun addini wanda yakan jawo kashe-kashe. Yusuf Ibrahim ya kara da cewa idan an yi tashin hankali sun gane su matasa ne ke da asara. Dalili ke nan matasan suka gani ya kamata su hada kai su kawo karshen tashin hankali.

Wani malamin addinin Musulunci Malam Tanimu Yusuf ya ce tattaunawa tsakanin Musulmai da Kiristoci ba zata tsaya wurin cin abinci ba kawai. Ya ce tattaunawa tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba abu ne wanda Musulunci ya karfafa shi domin ta haka ne a ke samun fahimtar juna. Ta haka ne a ke samun lafiya kuma ta haka ne addinan su ke fahimtar junansu. Ya ce a littafan addinan biyu akwai abubuwan da aka ce su kauce ma ko su kiyayesu. Idan ana taron fahimtar juna an bi abubuwan dake cikin littafan kamar aikata gaskiya da rikon amana da neman zaman lafiya to Najeriya zata kasance cikin zaman lafiya da cigaba.

Ga karin bayani.
XS
SM
MD
LG