Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Mayakan Sakai Ta MEND Tana Kashedi Ga Gwamnatin Najeriya


Wasu Mayakan sa kai kenan ke sintiri cikin kududdufan Naija-Delta a Nijeriya. (File photo)
Wasu Mayakan sa kai kenan ke sintiri cikin kududdufan Naija-Delta a Nijeriya. (File photo)

Kungiyar ‘yan yakin sa kai ta MEND a yankin Niger Delta na Nigeria tayi ikirarin cewa ita keda alhakin harin da aka kaiwa wata masa’antar mai a ranar talata a yankin na Niger Delta.

Kungiyar ‘yan yakin sa kai ta MEND a yankin Niger Delta na Nigeria, tayi ikirarin cewa ita keda alhakin harin da aka kaiwa wata masa’antar mai a ranar talata a yankin na Niger Delta.

Kungiyar MEND wacce itace babbar kungiyar yan yakin sa kai a kudancin Nigeria, a wata sanarwar data aika ta hanyar aika sakonin e-mail ga kafofin yada labaru a jiya Laraba, tace mayakanta ne suka kai harin.

Kungiyar tace hari da kuma hare hare makamancin na ranar talata, tuni ne ga gwamnatin cewa kada tayi wasa da irin gargadin da take gabatarwa.

Tunda farko jami’an tsaro sunce masana’antar dake jihar Bayelsa mallakin kamfanin mai na Agip a ranar talata da dare aka kai mata hari. Ba’a dai bada rahoton ko wani ya jikatta ba.

A kwanan nan kungiyar MEND ta bada sanarwar cewa zata kai hare haren bama bamai akan masa’antu da kamfanonin mai a duk fadin kasar. Haka kuma ta yi wa mutane kashedin cewa su nisanci duk wasu tarurrukan siyasa.

Kungiyar MEND tayi shekaru tana kaiwa masa’antun-mai hare hare. Yawancin diyan kungiyar a shekara ta dubu biyu da tara, suka bada makamansu karkashin wani shirin ahuwa na gwamnati, to amma har yanzu akwai wasu ‘yan yakin sa kai suke ci gaba da kai hare hare.

XS
SM
MD
LG