Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Saman Nijeriya Kirar Jet Ya Fadi, Matukin Ya Mutu


Wannan ba hoton jirgin da ya yi hadari yau din ba ne. Wannan hoton wani jirgin da kwanan baya ya yi hadari a filin jirgin saman Bauchin arewacin Nijeriya kenan bayan da ya yi karo da wasu dabbobi. (File photo)

Hukumar Jiragen Saman Yakin Nijeriya ta ce daya daga cikin jiragenta kirar jet ya rikito a kusa birnin Kano na arewacin Nijeriya, ya hallaka matukin.

Hukumar Jiragen Saman Yakin Nijeriya ta ce daya daga cikin jiragenta kirar jet ya rikito a kusa birnin Kano na arewacin Nijeriya, ya hallaka matukin.

Wani mai magana da yawun hukumar Jiragen Saman Yakin mai suna Yusuf Anas, ya ce jirgin, samfurin F7 kirar China ya fadi a yayin da ake koyon tuki da shi a yau Talata a Filin Jirgin saman Kano.

Rahotanni daga inda abin ya auku sun ce jirgin ya fado a yayin sauka a lawalin saukar sannan ya kama da wuta.

Ba a sami bayanin musabbabin faduwar jirgin ba. Hukumar jiragen ta ce ta fara bincike.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG