Accessibility links

Kungiyar MEND Ta Ce Ita Ta Kai Hari Ta Kashe 'Yan Sanda Hudu


'Ya'yan tsohuwar kungiyar Niger Delta Vigilante Group ta Ateke Tom

Wannan shi ne karo na biyu cikin wata guda da kungiyar tsageran yankin Niger Delta ta ek daukar alhakin kai farmaki a yankin na kudancin Najeriya

Wata kungiyar tsagera a yankin Niger Delta ta dauki alhakin kashe ‘yan sanda hudu a wani harin da aka kai kan wurin da ake binciken mutane da ababen hawa a kan hanya.

Kungiyar MEND ta fada cikin wata sanarwar da ta bayar yau jumma’a cewa ita ce ta kai harin na jiya alhamis a kan wurin binciken na ‘yan sandan ruwa a Jihar Bayelsa dake kudancin kasar. Wannan shi ne hari na biyu da kungiyar take daukar alhakin kaiwa a cikin wannan watan.

Har ila yau kungiyar ta ce tana tuntubar mutanen da suka sace ma’aikata guda uku na wani jirgin ruwan kasar Netherlands ko Holland wanda hukumomi suka ce ‘yan fashin teku sun far wa ranar talata a kusa da gabar Najeriya.

Ta ce wadanda suka sace ma’aikatan sun yi tayin mika su ga ita kungiyar ta MEND, ta kuma ce lafiyarsu kalau.

Kungiyar MEND ta yi ta kai hari a kan cibiyoyin kamfanonin mai na kasashen waje kafin akasarin membobinta su sanya hannu a kan yarjejeniyar ahuwa da gwamnatin Najeriya a shekarar 2009.

Kungiyar ta yi gargadi a cikin sanarwarta ta yau jumma’a cewa zata kai farmaki a kan jiragen ruwan kamfanonin mai dake aiki a cikin tekun gabar Najeriya. Ta ce zata cilla rokoki tare da kona duk wani jirgin ruwan da ya “ki bayar da hadin kai” ya shiga cikin aikin dakile yin fashi a ruwan tekun yankin.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG