Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talata Kotun Kolin Amurka Ta Saurari karar Wasu 'Yan Niger Delta, Kan Kamfanin Shell


Kamfanin mai na Shell

Shekaru 17 bayan gwamnatin mulkin sojan Najeriya ta aiwatarda hukuncin kisa kan masu gwagwarmayar kare muhalli su tara daga yankin Ogoni mai arzikin mai.

Shekaru 17 bayan gwamnatin mulkin sojan Najeriya ta aiwatarda hukuncin kisa kan masu gwagwarmayar kare muhalli su tara daga yankin Ogoni mai arzikin mai, tareda goyon bayan jami’an kamfanin mai na Shell yanzu shari’ar tana gaban kotun kolin Amurka. Jiya talata alkalan kotun kolin Amurka su tara, suka saurari mastayar bangarorin biyu kan ko ana iya gurfanarda kamfanin Shell a a Amurka.

Uwargidan daya daga cikin masu gwagwarmayar da suke yiwa Shell zanga-zanga da aka kashe a 1995, Esther kiobel ce ta shigarda kara kan kamfanin Dutch Shell. A 2009 kamfanin Shell ya cimma yarjejeniya a wajen kotu dab da za’a fara shari’a a New York, ta biya dala milyan 15 da rabi.

A lokacin zaman kotun ranar talata,daya daga cikin alkalan kotun kolin, Samuel Alito, yana mamakin yadda shari’ar ta baya bayan ake sauraronta a Washington, alhali wacce ta shigarda kara da kamfanin duka ba Amurkawa bane.

Shi kuma alkali Anthony Kennedy, wadda galibi shi yake kada kuri’ar da take raba gardama a kararraki dake gaban kotun, ya bayyana damuwar cewa idan kotun ta goyi bayan wacce ta shigarda kara, hakan sai bude kofa ga kamfanonin Amurka a ketare.

‘Yan gwagwarmaya daga Najeriya suna murnar kotun kolin Amurka ta saurari kararda suka shigar, kuma sun dauki alkawarin ci gaba da fafatawa koda wani irin hukunci kotun kolin ya yanke, wadda ake sa ran kotun kolin zata bayyana a karshen watan Yuni. Sunce suna son a saurari shari’ar a Amurka domin basa jin zasu sami adalci idan aka yi shari’ar a kotunan Najeriya.

Marco Simons, darektan harkokin shari’a na kungiyar rajin kare muhalli ta kasa da kasa dake nan Washington, wadda yake goyon bayan hukunta kamfanoni, yace bai karaya ba.

Wadanda suka shigarda karar suna kokarin amfani da wata tsohuwar dokar Amurka ta 1789, wacce ta baiwa kotunan Amurka damar sauraron kararda ‘yan kasashen waje suka kawo gabansu da suka sabawa dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyoy d a Amurka ta kulla. Abin tambaya anan shine ko ana iya amfani da wan nan doka kan kamfanoni.

Lauyar kamfanin Shell, Kathleen Sullivan ta sha nanatawa alkalan kotun kolin Amurkan cewa kotun taki amincewa da wan nan karar saboda ba’a babu haka a dokokin kasa da kasa ko irin wan nan shari’a da aka gudanar a baya.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG