Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Miyyati ta La’anci Kisan da Aka Yi Wa ‘Ya’yanta


Fulani makiyaya
Fulani makiyaya

Kungiyar Fulani makiyaya a Najeria ta Miyyati a jihar Oyo, ta lanci kisan da aka yiwa ‘ya’yanta uku da gangan, kuma kungiyar ta nemi da Gwamnati ta gaggauta yin wani abu a kan haka.

Yara ukun da aka kashe masu kiwon shanu ne, kuma maigidansu Alhaji Yuni. A cewarshi kabilanci ne yasa aka kashe su. “Kabilanci ne masu gonaki suka yi musu. Inda suke daji ne, wajen shan ruwa ne.”

Shugaban kungiyar na jihar Oyo Alhaji Yakubu Ganyo shine ya fadi a ganawar da yayi da Muryar Amurka. “Mun yi Allah wadai ga abunda yake faruwa ga ‘yan uwanmu makiyaya, da ake kashe su kowani lokaci.”

Shugaban ya kara da cewa “Wallahi gwamnati tazo ta dauki mataki, yanda ya kamata don Fulani sun gaji. Ana kashe mu babu dalili, kuma gwamnati bata dauki mataki ba.”

Wadannan yara dai an kashe su ne a Karamar Hukumar Atisbo a jihar Oyo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG