Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar NLC Na Adawa Ga Batun Sayar Da Kaddarorin Gwamnatin Najeriya


Kungiyar Kwadago

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC zata bayyana matakan adawa da batun sayar da kadarorin gwamnatin kasar a yau Talata.

Inda hukumar Tarawa da raba kudaden shiga ta Najeriyar ta nuna rashin amincewa ga kiran sayar da kamfanin iskar gas na Najeriya ga ‘yan kasuwa don amfani da kudin wajen raya tattalin arziki. Mukaddashin shugaban hukumar Shattima Umar Abba Gana, yace raya kamfanin ya ci gaba da aiki a matsayin mallakar gwamnatin Najeriya ya fi alheri.

Abba Gana, ya bayar da shawarar Najeriya ta nemo lamani don samun kudin aiki maimakon sayar da kadarori masu muhimmanci, inda yace jama’ar Najeriya na son tattalin arzikin kasar ya rinka bunkasa, amma idan ana sayar da su ta yaya zasu bunkasa.

Mukaddashin shugaban hukumar tara kudaden ya bukaci masu zuba jari da duk masu hannu da shuni su kafa sabbin kamfanoni maimakon neman sayan kamfanoni mallakar daukacin al’ummar Najeriya. Tuni dai ministan kasafin kudin Najeriya Udoma Udo Udoma, yace sayar da kamfanonin ba zai shafi mafiya muhimmanci ba.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG