Da ya ke bayani ma wakilinmu a jihar Naija, Mustapha Nasiru Batsari, Shugaban kungiyar, Malam Nura Hashimu ya ce manufar kungiyar ita ce ta cusa sha'awar zaman lafiya a zukatan al'umma ta wajen karrama wadanda su ka taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya.
Wasu da su ka amfana da kungiyar sun yaba mata da kokarin inganta daawah ta hanyoyin da Musulunci ya amince da su masu tabbatar da zaman lafiya. Haka zalika, wasu dalibai sun ce komfutocin da aka ba su za su taimaka wajen daukaka ilimi.