Accessibility links

An Hallaka Mutane 39 A Garin Wukari


Mata da yara sun fi cutuwa a rikice-rikicen da ke faruwa a Nijeriya

An hallaka kimanin mutane 39 a garin Wukari na jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Nijeriya

A cewar hukumomi, kimanin mutane 39 ne aka hallaka baya ga salwantar dukiyoyi masu dinbin yawa a rikicin da ya biyo bayan hidimar binne wani basarake dan kabilar Jikun a a garin Wukari na jihar Taraba. Kodayake ma jama'ar garin na cewa adadin mace-macen ya fi yadda hukumomin ke bayyanawa.

Wakilinmu na jihar Adamawa Ibrahim Abdul'aziz ya yi hira da wani da abin ya rutsa da shi, wanda ya bayyana cewa abin ya yi muni. Kuma kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar Taraba ASP Joseph Kwaje, wanda ya tabbatar da adadin da hukumomi su ka bayar ga wakilinmu, ya ce hankula sun kwanta a hanzu hakan. Kodayake wakilin namu ya ruwaito mutanen gari na dari-dari.
XS
SM
MD
LG