Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar WiJAfrica Ta Sanya Sunan Grace Alheri Abdu A Jerin Sunayen Mata ‘Yan Jarida Da Suka Yi Fice A Africa A 2023


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Kungiyar karfafa ‘yan jarida mata a Afirka da ake kira Women In Journalism Africa ko WiJAfrica a takaice, ta fitar da sunayen mata 25 da suka yi fice da kuma gogewa a aikin jarida a shekarar 2023.

Jerin sunayen da kungiyar ta WiJAfrica ke fitarwa a duk shekara na zaman wata babbar karramawa ga mata ‘yan jarida na nahiyar da sunayensu suka fito.

Babbar Editar sashen Hausa na Muryar Amurka Grace Alheri Abdu, na daga cikin ‘yan jarida mata ashirin da biyar da kungiyar ta bayyana a matsayin wadanda suka yi fice a Afirka a bana, wajen kwarewa, jajircewa, da bayar da rahotanni masu tasiri a rayuwar jama’a.

'Yar Majalisar wakilan Amurka Frederica Wilson tare da Grace Alheri Abdu ta VOA
'Yar Majalisar wakilan Amurka Frederica Wilson tare da Grace Alheri Abdu ta VOA

Wannan dai shi ne karo na biyu da Grace Alheri Abdu ta samu wannan karramawar, kamar yadda ta bayyana a wata hira da Muryar Amurka. Ta bayyana jin dadinta game da karramawar, tana mai cewa hakan na tasiri sosai a aikin jarida musamman wajen karfafa gwiwar mata.

Grace ta ce mata da yawa na fuskantar kalubale sosai wajen gudanar da aikinsu a Afirka, ta kuma kara da jan hankalin mata da matasa masu sha’awar aikin jarida da su ba da himma.

Wannan dai na zuwa ne gabanin bikin ranar 'yancin ‘yan jarida ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, wato ranar 3 ga watan Mayu na kowacce shekara.

Grace Alheri Abdu (VOA Housa)
Grace Alheri Abdu (VOA Housa)

Daga cikin sauran matan da suka samu karramawar har da Kadaria Ahmed ta gidan rediyon RadioNow 95.3FM, da Bilkisu Labaran ma’aikaciyar BBC.

Saurari hirar da Zahra Fagge ta yi da Grace Abdu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:52 0:00

XS
SM
MD
LG