Barrista Dalung yace “yanzu da nake maka magana, ina cikin garin Yola, kowane dan arewa dake wadannan jihohi guda uku, wanda yake da bayani na cin zarafi daga jami’an tsaro, ko ma wanene, da keta hakkin bil adama, da laifukkan yaki, da kwashe-kwashen dukiya, a kawo mana wannan ofis. Muna kan tattara bayanai domin wannan kungiyar zata kai karar gwamnatin Tarayya a kotun duniya na hukunta manyan laifuka, domin muna zarginta da cin amanar ranstuwar da tayi.
Wannan na zuwa ne, a lokacin da daya daga ciking gwamnonin dokar-ta-baci, wato Jihar Adamawa Murtala Nyako yake haramar kai gwamnatin Tarayyar kara a kotun bin Kadin manyan laifuka ta ICC.
“Yanzu muna so, duk wanda aka kashe masa, wani nashi, don Allah Ya tsaya, zamuyi da kanmu, zamu kira kungiyoyin kasa da kasa, da kungiyoyin kare hakkin bil adama, da kungiyar agaji, akan a bayar da sunayen wadanda aka kashe, da hotunansu, dole mu hada takardunnan, duk wadanda suka saka mu gaba kam, sai mun kaisu ‘The Hague’, kotun Majalisar Dinkin Duniya mai bin kadin manyan laifuka bisa zargin kisa kare dangi. Saboda haka, wannan yanzu abunda zamu saka a gaba kennan,” a cewar Admiral Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa.
Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Nyako, tana mai cewa kalamunshi basu da tushe balle makama, kuma so yake ya raba kan 'yan Najeriya.
Hukumar kare hakkin bil adama, ta Human Rights Watch tayi kiran a gudanar da bincike tare da neman hukunta sojoji da ‘yan sandan da suka aikata laifin keta hakkin bil adama. Haka kuma, hukumar ta kalubalanci gwamnatin Najeriyan gameda yin sakaci wajen kula da sha’anin Boko Haram.
Idan ba’a mance ba, babbar mai shigar da kara a kotun duniya Fatou Bensouda, ta bayyana cewa kotun a shirye take ta binciki batutuwan dake da nasaba da rigingimun Boko Haram.
An kwashe tsawon lokaci ana fama da hare-haren da suka jawo asarar rayuka da dukiyoyi a arewacin Najeriya, da ake zargin kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, tare kuma da zargin jami’an tsaro wajen gallazawa tare ma da kisan mutanen da basu ji ba, basu gani ba.