Accessibility links

Jami’an tsaron hadin gwiwa, sojoji da ‘yan sanda, da ‘yan sandan sirri, wato SSS da kuma jami’an shige da fice sun kai wani farmaki Asabar dinnan, domin kama al-ummomin Hausawa dake zaune a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom, a yankin Niger-Delta.

A cikin wadanda sumamen ya shafa, harda Hausawa masu jibi da kasashen ketare kamar Chadi, Kamaru da Nijar, saboda lamarin ‘tsaro’ dake addabar Najeriya, musamman hare-haren boma-bomai dake addabar wasu sassan kasar.

Jami’an tsaron na hadin gwiwa, sunyi awon gaba da darurwan al-ummomin arewacin Najeriya, a cikin wasu manyan motoci zuwa wani babban filin wasa dake birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom, domin gudanar da wani bincike na musamman, domin tantance wanda hukumar Shige da Ficen Najeriya ke jagorantar tantancewa.

Rahotanni masu karo da juna sunce an samu wasu bayanan sirri dake cewar an boye wasu bindigogi da boma-bomai a wasu kasuwanni da al-ummomin arewacin Najeriya ke gudanar da harkokinsu a sassa daban-daban na birnin na Uyo, a jihar ta Akwa Ibom.

Mallam Muhammadu Adamu, shine babban limamin Massallacin Juma’a na Uyo, a Jihar Akwa Ibom, wanda wakilin Sashen Hausa Lamido Abubakar ya tuntuba domin jin karin bayani game da yadda lamarin ya faru.

“Kwarai da gaske jami’an tsaro ne, duk wuraren da jama’ar mu suke, harkoki na kasuwancinsu, jami’an tsaro sun kewaye wurun gaba daya. Suka dinga diban mutane, ana zuba su cikin motoci,” a cewar Mallam Adamu. “To amma da muka nemi bayani sai shuwagabannin suka ce a’a ba wani abu bane, saboda abubuwan da suke faruwa a cikin kasa lamarin tsaro shiyasa, kuma ta ganin baki na ta shigowa garin, saboda kara gaba, shiyasa suke bincikar mutane.”

To sai dai kuma, wasu bayanai na cewa wannan kame bashi na nasaba da batun zargin boye bindigogi da boma-bomai.

Jami’an tsaro su tabbatarwa Muryar Amurka cewa wannan aiki ne na tantance ‘yan Najeriya, da kuma ‘yan kasashen ketare, domin gano wadanda ke zaune ba bisa ka’ida ba, bisa la’akari da matsalolin tsaron dake addabar Najeriya.

Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin jami’an Shige da Fice a Jihar Akwa Ibom, dangane da wannan lamarin, amma babu nasara.

Ire-iren wadannan kame-kame da bincike na cigaba da faruwa a wassu sassa inda ake da zaman lafiya a Najeriya, yayinda jama'ar arewacin kasar, musamman arewa maso gabashin kasar ke kukan rashin tsaro a jihohinsu.

XS
SM
MD
LG