Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Sun Yi Bitar Halin Da Ake Ciki Game Da Bauta A Nijer


A yayinda ake shagulgulan tunawa da ranar yaki da bauta ta duniya a yau 2 ga watan disamba kungiyoyin yaki da bauta a jamhuriyar Nijer sun yi bitar halin da ake ciki game da wannan al’amari shekaru 70 bayan wannan yunkuri na kawo karshen wannan dabi’a.

Jamhuriyar Nijer na daga cikin kasashen da suka yi kaurin suna a yankin Afrika ta yamma akan maganar bauta a bisa la’akari da bayanan da ke nunin yadda a wasu yankunan kasar ake ci gaba da aikata wannan haramataciyar dabi’a lamarin da ya sa a shekarun baya kungiyar TImidiria da wasu kawayenta suka daura damanar magance wannan matsala, sai dai alamu na nunin har yanzu da sauran rina a kaba inji sakataren kungiyar Ali Bouzou.

Wannan al’amari dake ci gaba da turjewa doka wani abu ne da ke shafar tsarin zamantakewar al’uma inji Masani a wannan fanni Dr Sani Yahaya Janjouna.

Jinsin mata ya fi dandana kudar wannan haramtaciyar dabi’a wace a wani zubin kan shafi rayuwar yaran da matan da suka tsinci kansu cikin halin bauta kamar yadda tamabarar masarautar Keltemet Mme Almansour Hindou ta bayana wa Muryar Amurka.

Dukkan gwa;notocin da suka mulki Nijer sun sha alwashin kawo karshen bauta a wannan kasa ta hanyar dokokin da aka kafa shekaru da dama sai dai kawo yanzu abin na nan kamar a nan magani kai yana kaba lamarin da kungiyar Timidria ta dora alhakinsa akan raunin wadanan dokoki a yayinda hukumomI da kansu ke dari darin shiga wannan yaki gadan gadan gudun kada a sami sabani a tsakaninsu da sarakunan gargajiyar dake ci gaba da bautar da mutane a yanzu haka lamarin da ya sa a kowane lakoci Timidria kan garzayawa kotun ECOWAS a maimakon ta ja shara’a a nan gida,

Saurari cikakken rahaton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00


XS
SM
MD
LG