Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin ma'aikatan kasar Faransa sun tsaida shawarar shiga wata zanga zanga ta kwana biyu


Zanga Zangar Dalibai a kasar Faransa.

Kungiyoyin ma’aikatan kasar Faransa sun yi kira da a ci gaba da wani sabon yajin aikin gama gari na kwana biyu domin ci gaba da nuna adawa da garambawul a tsarin fensho na kasar.

Kungiyoyin ma’aikatan kasar Faransa sun yi kira da a kara kwana biyu a yajin aikin gama gari na adawa da garambawul da ake shirin yiwa tsarin fensho na kasar. Shugabannin manyan kungiyoyin kwadago takwas sun sanar da shirin wani sabon yajin aiki na kwana biyu a ranakun 28 ga wannan watan na Oktoba da kuma shida ga watan gobe. Shugabannin dai sun dorawa gwamnatin alhakin sake shiga yajin aikin, sabili da kin sauraron jama’a. Nadin Preduant jami’ar kungiyar kodagon ta bayyana matukar gamsuwa da goyon bayan da suka samu daga jama’a, Bisa ga cewarta binciken ra’ayoyin jama’a ya nuna cewa kashi 79% na al’ummar kasar suna fata a ci gaba da tattaunawa da kungiyoyin ma’aikata. Yayinda kashi 65% na al'ummar kasar kuma, basu yarda da yadda shugaban kasar yake matsantawa kan batun ba. Masu zanga zanga a birnin Paris sun taru a harabar majalisar Dattijai jiya Alhamis, inda ake mahawara kan dokar ritayar da ta haddasa tarzomar. Masu zanga zangar sun ce suna yajin aiki ne sabili da gwamnati tana son mutane suyi ta aiki sai sun kai shekaru 67 kafin suyi ritaya, ba tare da samun wani kudin kirki ba.Shugaba Nicolas Sarkozy yaki mika wuya bori ya hau a matsin lambar da yake fuskanta daga jama’a. Bisa ga cewarsa, ana bukatar yiwa garambawul domin ceto tsarin daga talaucewa.

XS
SM
MD
LG