Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Ganyen Tabar Wiwi Na Naira Miliyan Dubu 51 A Kasar Mexico


Fakiti dubu 10 na ganyen tabar wiwi da jami'an tsaron Mexico suka kama, litinin 18 Oktoba, 2010 a birnin Tijuana dake bakin iyakar kasar da Amurka.

An kama wannan ton 105 na ganyen wiwin a birnin Tijuana dake bakin iyakar Mexico da Amurka a cikin fakiti dubu 10

Dakarun tsaro na kasar Mexico sun kama ton 105 na ganyen tabar Wiwi a birnin Tijuana dake bakin iyakar kasar da Amurka, a wani lamarin da aka bayyana a zaman kamun kwaya mafi girma cikin ‘yan shekarun nan a kasar.

Hukumomi sun ce an kama wannan ganyen tabar Wiwi jiya litinin a wasu samamen da ‘yan sanda da sojoji suka kai cikin wasu unguwanni uku, inda aka kama mutane 11. Janar Alfonso Duarte na rundunar sojojin Mexico yace farashin wannan ganyen tabar wiwi a kasuwa zai kai sama da dala miliyan 340, kimanin Naira miliyan dubu 51.

Wani sojan Mexico ya damko wani madugun fataken muggan kwayoyi, litinin 18 Oktoba 2010 a birnin Tijuana
Wani sojan Mexico ya damko wani madugun fataken muggan kwayoyi, litinin 18 Oktoba 2010 a birnin Tijuana

Duarte yace an kunshe wannan ganyen tabar wiwi a cikin fakiti dubu 10, aka yi rubuce-rubuce na batar da kama a jiki. Yace an kama ganyen tabar wiwin a daidai lokacin da ake shirye-shiryen sufurinsa domin rarrabawa a Amurka.

Sojojin kasar Mexico su na yin kare-jini biri-jini da gungun fataken muggan kwayoyi na kasar tun lokacin da shugaba Felipe Calderon ya hau mulki a shekarar 2006. An kashe mutane kusan dubu 30 tun lokacin da sojojin suka fara dirkakar fataken muggan kwayoyin.

XS
SM
MD
LG