Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matuka Manyan Motocin Dakon Kaya a Faransa Sun Cika Manyan Hanyoyin Faransa A Ci Gaba Da Zanga Zangar Kyamar Garambawul din Shirin Ritaya na Kasar


Matuka manyan motocin dakon kaya suka cika kan manyan hanyoyin faransa domin nuna rashin amincewarsu da shirin garambawul din fansho.

Hukumomin Faransa sun kama kai saboda gagarumar zanga zangar gama gari da ake sa ran ma'aikata zasu kaddamar ranar Talata, a ci gaba da matsin lamba kan hukumomin kasar.

Matuka manyan motocin dakon kaya a Faransa zasu cika manyan hanyoyi kuma su kashe kafa domin bayyana rashin goyon bayansu kan garambawul na shirin fanshon kasar.

Hukumomin kasar sun kama kai, saboda wani zagayen zanga zangar gama gari ranar Talata. Litinin, ma’aikatan matatun mai,daliban makarantun sakandare, maikatan jirgin kasa,da wasu ‘yan zanga zanga suna kokarin ci gaba da matsin lamba kan shirin shugaba Sarkozy na garambawul ga shirin ritayar kasar, da majalisar dattijan zata kada kuri’a akai cikin makon nan.

Ma’aikata suna kokarin shawo kan wakilan majalisar dattijan kasar a kuri’a da zasu kada ranar Laraba, shirin ya kunshi kara shekarun ritaya daga 60-62. Tuni majalisar wakilan kasar ta amince da kudurin cikin watan jiya,kuma ana jin majalisar dattijan ma zata amince da shi.

Daliban makarantun sakandare sun shiga zanga zangar ce cikin makon jiya, kuma sai da ‘yan sandan kwantarda tarzoma a wasu alkariyan Paris suka yi amfani da borkono mai sa hawaye ranar litinin,domin tarwatsa matasa da suka rufe fuskokinsu, suka cunnawa motoci da dama wuta,da lalata wuraren shiga motoci.

XS
SM
MD
LG