Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Mata Na Kalubalantar Shugaba Kiir Kan Raba Mukamai


Kungiyoyin mata sun ce, bangarorin da suka kafa gwamnatin hadin kai a Sudan ta Kudu sun saba yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 da aka farfado da ita wacce ta amince cewa a ba mata kashi 35 cikin 100 na mukaman gwamnatin da aka kafa.

Shugabar kungiyar mata ta South Sudan Women’s Bloc, Amer Manyok Deng, na daga cikin masu ruwa da tsaki a tattaunawar zaman lafiyar, ta kuma bukaci shugaban kasa Salva Kiir a jiya Alhamis da ya soke mukaman gwamnoni 8 na baya bayan nan da aka nada, wanda mace daya ce kacal a ciki.

Deng ta fadawa shirin Muryar Amurka na “South Sudan in Focus” cewa, idan shugaba Kiir ya ki, ya kamata ya nemi mafita da za ta yi daidai da kashi 35 cikin 100 da aka ware saboda a samu wakilcin mata a dukkan matakan gwamnati.

Bugu da kari, Deng ta ce rabi daga cikin majalisar ministoci shugaban kasa ya kamata su zama mata, kamar na mukamin kakakin majalisar dokoki ta rikon kwarya da kuma shugabar alkalai.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG