Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Mata na Kiran Sako Daliban Cibok


Hudu daga cikin dalibai mata 'yan makarantar Sakandaren Cibok da suka kwace daga hannun mahara, Afrilu, 23, 2014.
Hudu daga cikin dalibai mata 'yan makarantar Sakandaren Cibok da suka kwace daga hannun mahara, Afrilu, 23, 2014.

Iyayen daliban da aka sace a Makarantar Sakandare dake Cibok a jihar Borno sun yi taro inda suka yi kira ga 'yan ta'adda dasu sako 'ya'yan nasu su sama da 200 da aka sace.

Kungiyoyin mata da iyayen dalibai mata da aka sace a Cibok sun yi kira ga ‘yan ta’adda dasu dubi girman Allah su sako yaran da suka kwashe a makarantar Sakandare ta kwana inda yaran ke rubuta jarrabawar karshe.

Sun yi wanna kiran ne a wajen wani taro da suka yi da manema labarai a garin Maiduguri.

Iyayen na wadannan dalibai suna sanye da bakaken tufafine a wajen taron, kuma sun fashe da kuka lokacin da Farfesa Hauwa Abdu Biu, ke karanta jawabi a madadin sauran matan dake jihar.

Farfesa Hauwa Biu tace ”duk kanmu a zaman mu na iyaye mata idan muka kwanta bamu iya yin barci saboda muna sa kanmu a matsayin iyaye yaran domin bamu san wani hali yaran nan suke ciki ba."

Ita kuma kwamishinar ma’aikatar masana’antu Dr. Asabe Bashir cewa tayi “ina halartan taron ne a matsayi na uwa, ba kwamishina ba, domin duk mata ya kamata muyi kuka da abunda ya faru kuma karfin mu ya kasa da yake ba bindiga muke dashi ba, da zamu je mu kwato yaran."

Dakta Aishatu Yusuf Gulde, shugaban kungiyar kare hakkin mata da ake kira WRAPA ta nuna nata alhinin bisa ga faruwar wannan lamari, inda ma tace ”arewa dama mata nawa suke samu ci gaba mu kalilan ne, kowa yana fita gwamnati da kungiyoyi suna maganar ‘ya’ya mata ina maganar ‘ya’ya mata, idan wadanda suka samu suka je makarantar gwamnati ta na bari ana kwashesu."

Mafi yawancin wadanda sukayi magana a zauren taron, sun yi suna kuka da share hawaye.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG