Accessibility links

Yayin da gwamnan Borno ya kai ziyara a garin Cibok domin ya jajantawa iyayen da aka sace 'ya'yansu, iyayen su shaidawa gwamnan cewa yara 234 aka sace sabanin 129 da makarantar ta sha ambata.

Iyayen 'yan matan da aka sace daga garin Cibok sun shaidawa gwamnan Borno cewa adadin 'ya'yan nasu da aka sace 234 ne ba 129 ba kamar yadda makarantar ta sha fada. Amma 39 sun samu kubuta.

Iyayen sun shaidawa gwamna Kashim Shettima ne lokacin da ya kai zaiyara garin Cibok domin gane ma idanunsa irin barnar da aka yi a makarantar da kuma jajantawa iyayen.

Gwamnan ya soma da yiwa iyayen juyayin abun da ya faru. Yayi alkawarin nemo yaran domin mayar dasu wurin iyayensu. Lokacin da yake yiwa iyayen yaran jawabi kwalla na fitowa daga idanunsa. Yace abun da ya samesu ya shafi duk mutumin kasar nan. Yace yara ne da basu san hawa ba basu san sauka ba sun zo neman ilimi ne. Yace jami'an tsaro suna gwargwadon karfinsu domin gano yaran. Yace kawo yanzu ma suna gwagwarmaya da 'yan ta'adan. Gwamnan ya kara da cewa bai cancanta ya bayar da bayani fiye da haka ba. Ya baiwa iyayen hakuri da cewa matsifa ce ta fado akan jihar.

Shi ma Sanata Ali Ndume daga mazabar kudancin Borno ya yiwa iyayen jawabi cikin jimami da tausayawa. Yace dalilin da yasa suka kai ziyara domin su sani suna tare da su ne. Yace "abun da ya same ku ya same mu. Me nene shugaba idan jama'arsa suna cikin kunci? Me nene shugaba idan kai kana da lafiya wadanda kake shugabanci basu da zaman lafiya?" Yace Allah "ya jarabcemu da wannan shugabanci" Yace su din ma babu abun da zasu iya yi saidai su koma ga Allah su rokeshi ya kawo sauki.

Wasu daga cikin iyayen sun bayyana abun al'ajabi da suka gani lokacin da suka je farautar 'ya'yansu cikin daji. Suka ce sun dauki babura dari da hamsin suka nufi jejin. Sun tarar da gidaje biyu kawai da wasu mata da dama. Bayan sun yi tafiyar kilomita ashirin da biyar basu ga rana ba. Sun kai wata gada da aka yi da itatuwa. Sun bi karkashin gadar har suka kaiga wani tsoho wanda ya fada masu cewa ranar da aka sace 'ya'yansu sun tsaya a bakin gadar kusan minti goma sha biyar. Daga bisani ya nuna masu wani wuri yace idan sun kai wurin ba zasu fita da rai ba.

Daga bisani sun godewa gwamnan jihar da kokarin da yake yi. Sun gargaeshi kada ya karaya amma ya samu jami'an tsaro da zasu kubuto masu 'ya'yansu.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
XS
SM
MD
LG