Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura Ta Fara Lafawa a Aba Jihar Abian Najeriya


Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB
Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB

Bayan an kwashe kusan mako daya sojoji da 'yan rajin kafa kasar Biafra, IPOB, suna gwabzawa da juna a birnin Aba dake jihar Abia, yanzu kura ta fara lafawa lamura sun soma komawa kamar da

Yanzu dai, lamura sun fara lafawa a biranen Aba da Umuahia dake jihar Abia, yankin kudu-maso-gabashin Najeriya, bayan kusan mako guda da aka kwashe ana gwabzawa tsakanin dakarun sojin Najeriya da ‘yan kungiyar IPOB, dake rajin kafa kasar Biafra.

Sakamakon haka ne ake kyautata zaton cewa dakarun sojin da aka turo don kwantar da rigingimun, zasu bar jihar yau Juma’a, bayan hedkwatar sojin kasar ta amince da yin hakan jiya Alhamis.

Na dai tuntubi wasu Hausawa mazau nan birnin Aba, don jin yadda al’amura ke kasancewa.

Usman Bello yace lallai da alamun kura ta lafa.

Wani mai suna Jude Udeachara mazaunin Ogbor Hill, ya shaida mini cewa natsuwa ta fara shimfida tabarma a birnin Aba.

Yace komai ya lafa a birnin kuma babu wata damuwa.

Alamomi dai na nuna cewa kamar rikice-rikicen ne suka janyo tsige Mista Adeleye Oyebade daga matsayin kwamishinan rundunar ‘yansandan jihar jiya, aka kuma turo Mr Anthony Ogbizi ya maye gurbinsa.

A daidai lokacin tura wannan rahoton, al’ummomin biranen Enugu da Awka da Onitsha da Owerri da kuma Abakaliki da Okigwe na cigaba da tafiyar da harkokinsu ba tare da wata takura ko tsangwama ba.

Ga rahoton Alphonsus Okoroigwe da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG