Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura ta lafa a Maza dake cikin karamar hukumar Jos ta arewa


Masana kimiyya a Jami’ar Arizona dake nan Amurka sun sakewa sauro fasalin haliita ta yadda ba zai iya dauka da yadar cutar zazzabin cizon sauro.

Kura ta lafa a kauyen Maza dake cikin karamar hukumar Jos ta arewa a tsakiyar Najeriya,bayan da wasu mahara suka kashe akalla mutane takwas.

Hukumomi sun ce mutanen da suka kai farmakin, sun yi amfani da adduna da wukake, kuma sun kona wata majami’a a kauyen da akasarin mazauna cikinsa kiristoci ne, kusa da Jos. Wan nan tarzomar ta zo ne dab da gama wata mummunar arangama a garin wukari dake gabashin kasar, har aka kashe akalla mutane hudu, a fada tsakanin musulmi da kirista. Tarzoma bisa sabanin akida ta halaka darururwan mutane a tsakiyar kasar. A arewacin Najeriya dai muslmi ne suke da rinjaye, a kudanci kuma kirista.

XS
SM
MD
LG