Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma watau ECOWAS ta kafa wani kwamiti da zai sa ido a kan shige da ficen mutane da kuma kayayyaki don tabbatar da ganin matafiya na samun gudanar da harkokinsu ba tare da samun tsaiko ba.
Duk da wannan matakin kafa kwamitin mai sa ido a kan wannan batu, lamarin yana kara huskantar turjiya daga jami’ai a kan iyakokin kasashen. Lawali Shaibu shine Kwamishinan ECOWAS kuma yayi Karin haske kan wannan lamari a wurin wani taron bita da aka yi Niamey.
Yan kasuwa masu zirga zirga da wannan al’amari yafi shafa, sun ce wannan hana ruwa gudun yana jawowa koma baya ga tattalin arzikin yankin baki daya. Hakan yasa yan kasuwa suna bijirewa gayyatar da kungiyar ECOWAS, saboda a cewarsu zaman bashi da amfani.
Facebook Forum