Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Kula Da Bangaren Wutar Lantarki Na Majalisar Wakilai Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Rasa Wuta A Abuja


Magaji Daú Aliyu

Tirka tirkar da ta faru har aka rasa wuta a babban birnin tarrayya da wasu Jihohi 5 a kwanakin baya ya fusatar da Kwamitin Kula da Bangaren Wutar Lantarki ta Majalisar Wakilai.

Hakan ya sa ya sha alwashin kawo karshen rudamin da ake samu a wannan fannin.ta hanyar binciko gaskiyar abin da ya wakana a lokacin da aka sayar da kamfanonin wutar lantarki a kasar.

To saidai Kwararru na cewa ba girin girin ba, ta yi mai.

Wanan rudani da ya jawo har aka sauya Shugabanni a Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja, ya samo asali ne daga wata takkadama da ta faru har Ma'áikatan Kamfanin suka shiga wani yajin aiki da gwamnati ta ce abin kunya ne a gare ta idan aka yi la'ákari da makudan kudade da aka zuba a fannin wutar lantarki.

Wani abu da ya sa aka rushe Hukumar AEDC ta hanyar shirin BPE ( Bureau of Public Enterprises) aka maye gurbinta da wata sabuwar tawagar riko da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta kafa, kamar yadda Shugaban Kwamitin Kula da Bangaren Wutar Lantarki a Majalisar Wakilai Magaji Daú Aliyu yayi karin haske.

Magaji ya ce wannan al'ámári babu hanun Shugaba Mohammadu Buhari a ciki kamar yadda aka yi hasashe da farko, rikicin yana tsakanin wadanda suka sayi Kamfanonin ne da wadanda ke gudanar da su. Magaji ya ce Gwamnati tana da kashi 40 cikin dari, sanan masu zuba jari masu zaman kansu a kamfanonin ke rike da kashi 60 cikin 100 na hanun jarin. Magaji ya ce kamfanin ba shi da kudi, yana rike da hakkokin ma'áikatan , wanda ba a iya biya ba na tsawon lokaci.

Shi ma daya cikin ýan kwamitin, Abubakar Yahaya Kusada ya ce wannan batu na gyarar wutar lantarki a kasar ya dauki tsawon lokaci amma yanzu za a yi wa tukkar hanci

Kusada ya ce tun zamanin Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa Ýar'ádua ne ake ta kai ruwa rana, amma har yanzu abin bai yi kai ba. Kusada ya ce Majalisa za ta yi binciken kwakwaf a wannan karon.

To saidai Mai fashin baki a al'ámuran yau da kullum kuma tsohon Mukadashin Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasar, Komred Isa Tijjani yana ganin an dade ana bincike a fannin wutar lantarki amma ba a samun mafita ba, saboda wasu dalilai na daban.

Isa ya ce ba a samun nasara a binciken da ya ki ci ya ki cinyewa , saboda manya ne suka sayar wa kansu da Kamfanonin saboda haka ba sa iya tsawata wa juna. Isa ya ce duk hanya ce ta azurta juna, kuma yana kara fitsarar cin hanci da rashawa a kasa. Isa ya ce da za a dage a yaki son zuciya, da an samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar ko da kadan ne, amma Majalisar ta zama 'yar anshin Shata.

Abin jira a gani shi ne yadda binciken zai kasance a Majalisar dokokin kasar bayan an kwashi shekaru da dama ana kai gauro ana kai mari akan batun samar da wadataccen wutar lantarki a kasar.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG