Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwana Guda Da Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Amurka


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Yayin da Amurkawa suke bukukuwan rantsar da shugaban kasa na arba’in da biyar, mutane a kasashen duniya sun gama wunin ta hanyoyi da dama.

A birnin Moscow, wani shagon sayar da sutura na sojin Rasha ya sa hoton Trump a wani katafaren akwatin wuta na tallace tallace, inda ya kuma tallata yiwa Amurkawa rangwame.

Trump ya bayyana karara a jawabinsa bayan rantsuwa cewa, gwamnatinsa zata bada fifiko wajen biyan bukatun Amurkawa.

Shekara da shekaru mun yi ta azurta masana’antun kasashen ketare a maimakon na Amurka, muka rika tallafawa rundunonin sojin wadansu kasashe, muna rage yawan dakarunmu a cikin gida, mun kare iyakokin wadansu kasashe yayin da muka ki kare namu.

A Afirka ta yamma, ra’ayoyi sun banbanta a Najeriya da Nijar. Amurkawa sun yabawa gwamnatin Barack Obama, muna yi masa addua, muna addu’a ga shugaba Donald Trump fatar Alheri a gwamnatinsa, a cewar Mallam Bello daga Nijar.

Duk da zafafan kalaman yakin neman zaben Trump, a cikin shekara guda da ta shige, addu’armu gareshi itace ya yi kokari ya hada kan kasashen duniya. Muna kuma fatar zai taimaki kasashe masu tasowa su habaka, a cewar wani ‘dan Najeriya.

Bukin rantsarwar ya samu halartar Amurkawa da kuma al’umman kasashen duniya da dama.

XS
SM
MD
LG