Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamishinonin Nyako da Mukaddashi Gwamnan Jihar Adamawa


Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa.

Mukaddashi gwamnan jihar, Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, yayi alkawari maido da ‘yayan jamiyar PDP da aka sace zuwa wata jamiya.

Yayin da guguwar tsige Murtala Nyako ke lafawa, batun da a yanzu yake kuno kai shine na canja sheka da ake zargin wasu da ada ke bagaren gwamna jihar suka soma yi.

Na baya-bayan nan shine ganawan da mukaddashi gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri yayi da kwamishinoni gwamnatin Nyako da aka rusa, batun da a yanzu ya fara jawo cece kuce.

Domin yayi da wasu ke zargin ziyaran da kwamishinonin, Murtala Nyako, suka kaiwa mukadashi gwamnan tafkar canja sheka su kuwa tsofin kwamishinoni da aka sauke ta bakin shugaban kungiyarsu Alhaji Aminu Iyawa yace “ ba gaskiya bane kamar yanda kuka sani nadin mu a matsayin kwamihinoni nadin ne na siyasa, abun daya kaimu shine neman hakkin mu.”

Tun farkon hawan sa, mukaddashi gwamnan jihar, Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, a jawabin daya yiwa shuwagabanin jamiyar PDP da suka ziyarce shi yayi alkawari maido da ‘yayan jamiyar PDP da aka sace zuwa wata jamiya.

Malama Binta Garba, shugabar jamiyar APC a jihar Adamawa, tace rashi tawakali ne kesa mutane canja sheka da zaran gwamnatisu ta fadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG