Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Jihar Adamawa ta Sha Bambam da Saura


Murtala Nyako, Gwamnan Jihar Adamawa.
Murtala Nyako, Gwamnan Jihar Adamawa.

Siyasar adamwa ta babanbanta da siyasar bangarori da yawa a Nijeirya.

A hirar da akayi da dakta Kabiru Mato, Yace “Jam’iyyar PDP baza ta fita daga zargin wannan tashin tashina da ke faruwa a jihar Adamawa ba, don in aka yi la’akari za a ga cewa yan majalisar jihar duk yan PDP ne.

A lokacin da Gwamana Murtala Nyako ya chanza sheka daga PDP (wanda bamu san dalili ba) zuwa APC, yan majalisar sa basu chanza ba. Biyar daga cikin yan majalisar da da suke jam’iyar APC, sai suma suka chanza sheka zuwa PDP”

Ya kuma kara da cewa siyasar Adamawa ta babanbanta da siyasar bangarori ban-da-ban a Najeriya, sai ya kasance duk wani mai hannu da shuni ko mai fada a aji ba ya jituwa da 'yan'uwansa. Duk wanda yake gaba, sai ya zama abokin gabar sauran. Amma a kano, sokoto da sauran jihohin da gwamnonisu suka bar ja’iyunsu, duk sai suka koma da kwansu da kwarkwatarsu.

XS
SM
MD
LG