Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru A Fannin Tsaro Na Mayarda Martani Ga Bukatar Kara Wa'adin Dokar-Ta-Baci


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Kwararru da kungiyoyin al'umma da kuma na kare hakkin bil Adama su na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan bukatar shugaba Goodluck Jonathan na kara wa'adin aiki da dokar-ta-baci

Kwararru a fannin ayyukan tsaro, da kungiyoyi na al'umma da na kare hakkin bil Adama, su na ci gaba da maida martanin da ya sha bambam kan bukatar da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya gabatar ga majalisun dokokin tarayya biyu na kasar kan kara wa'adin aiki da dokar-ta-baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Wa'adin yin aiki da dokar-ta-bacin ta yanzu zai kare a cikin mako mai zuwa.

Dr. Bawa Abdullahi Wase, kwararre a kan harkokin tsaron kasa, yace kara wa'adin ba shi ne zai magance wannan lamarin ba, domin kuwa duk da wannan dokar-ta-baci da ake aiki da ita, kusan kowane mako sai an samu labarin kashe-kashe.

Dr. Wase ya kuma ce tsinke layukan tarho da aka yi a akasarin wuraren da abin ke faruwa ya jefa tattalin arzikin yankin cikin mummunar matsala tare da dakushe hanyoyin samun abincin mutane masu yawa, a bayan tauye musu hanyar yin huldar zumunci da 'yan'uwansu dake wani wuri.

Yace kamata yayi a sauya dabarun takalar wannan batun, a kuma samo hanyoyin maslaha na kawo kasrhen tashin hankalin.

Shi ma dan rajin kare hakkin bil Adama, Barrister Solomon Dalung, yace muddin shugaba Jonathan yayi gaban kansa ya tsawaita aiki da dokar-ta-bacin ba tare da amincewar majalisun ba, zasu hada kai da jihohin da abin ya shafa su kai kara gaban kotu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz kan wannan...
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG