Accessibility links

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Tana Barazanar Tsige Gwamna Almakura

  • Aliyu Imam

Yan Najeriya suka shiga layi domin su kada kuri'a.

Wakilan Majalisar dokokin jihar suna zargin gwamna Almakura da kasa bin dokar kasa.

Wakilan majalisar dokokin jihar Nasarawa wadanda galibinsu ‘yan jam’iyyar PDP ne, suna barazanar zasu tsige gwamnan jihar Alhaji Umaru Tanko Almakura, wanda dan asalin jam’iyyar CPC ne kamin ta shiga sabuwar jam’iyyar hamayya ta APC.
Majalisar tana zargin gwamnan da amfani da wasu kudade da ba’a ksafta su ba, da suka hada da kudaden tallafin ambaliyar ruwa da wadansu. Lamari da majalisar take zargi acewarta ya bayyana fili sakamakon bincike da kwamitin kididdiga na majalisar ya gudanar.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Mohammed Baba Ebako ne ya tabbatar da haka, a hira da yayi da waliliyar Sashen Hausa Zainab Babaji.
Ebako yace gwamnan baya karbar shawara. Ya bada misali da shawarar da suka bayar na neman gwamnan ya sallami mai bashi shawara kan harkokin jam’iyun siyasa, Hajiya Hajara Dan Yaro, wacce wakilan suke zargi ta yi musu kazafi da ta shiga gidan rediyo tayi zargin cewa ana basu kudi.

Da aka tambayeshi ko da gaske ne wakilai 21 cikin 24 sun sanya hanu kan kudurin neman tsige gwamnan jihar? Wakili Mohammed Baba yace idan dai gwamnan bai natsu ya fara sauraronsu ba, to zasu yi amfani da sashi na 118 na tsarin mulkin Najeriya, wanda yace idan gwamna baya bin doka, to wakilan majalisa suna iya tsige shi.

Amma da take magana, Hajiya Hajara Dan Yaro, tace ‘yan majalisa basu bata dama ta kare kanta kan zargi da suka ce ta yi musu ba. Tace abunda ta fada shine ‘yan majalisa suna karbar milyan 10 kudin aikin mazabunsu bayan ko wani wata uku. Kuma basu ma tambayi haka ba lokacin da ta bayyana a gaban majalisa, maimakon haka suka dage kawai cewa tilas gwamna ya sallame ta daga bakin aiki. Amma gwamna Almakura bai yi haka.

Sai ranar jumma’a da ta shige ne a kashin kanta inji Hajiya Hajara, ta mika takardar ajiye aikin ta.

XS
SM
MD
LG