Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru A Harkokin Shari'a Na Ci Gaba Da Tsokaci Akan Kalaman Shugaba Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari A
Shugaba Muhammadu Buhari A

Masu fashin baki da masana a fannin tsaro a Najeriya sun yi nazarin kalaman Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce duk wanda aka kama ya sace akwatin zabe ya yi a bakin ransa, kalam sun kuma ja hankalin wasu da ke ganin ba daidai ba ne shugaban ya yi wannan huruci.

Bayan wannan hurucin shugaban kasa tuni har wasu jami'an tsaron sun ce a shirye suke su harbe duk wanda suka kama,wasu kuma na ganin ai kalaman nasa basu sabawa kundin tsarin mulki ba.

Wadannan kalamai da Shugaba Mohammadu Buhari ya yi na cewa a harbe duk wanda ya sace akwatin zabe ya haddasa muhawara mai tsanani a tsakanin kwararru a fanin tsaro da masana kundin tsarin mulkin kasa.

Kwararre a fanin kundin tsarin mulki Barista Yusha’u Waziri Mamman ya ce kashi 31 da kashi 32 na kundin tsarin mulki sun baiwa Shugaba Buhari hurumin daukan kowane mataki domin tsaron kasa, kuma banbancin abin da dokar zabe ta ce shi ne in an kama mai laifi a hukunta shi da sauri har na shekara uku.

Amma a nashi nazarin, shugaban kamfani tsaro na Bicon Sikuriti Kabiru Adamu ya ce daman can ana yiwa shugaba Buhari Kallon mai aiki da karfin sojoji kuma wadannan kalamai nasa sun nuna haka, gashi tuni har rundunan sojojin Fatakwol sun ce a shirye suke su bi wanan umurnin ka'in da na'in.

Amma ministan harkokin matasa da wasanni Barista Solomon Dalung, ya ce wandanan kalama na shugaba Buhari yana nuni da cewa Gwamnati ba ta yin shishigi a harkar zabe. Saboda haka hukumar zabe ta dauki matakin daga zaben ne da kanta ba tareda umurnin kowa ba.

Ga rahoton da wakiliyar sashin hausa Medina Dauda ta hada mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG